Gold Emmanuel 4 weeks ago

Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunci – Tinubu

Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunci – Tinubu

Shugaban kasa, Bola Tinubu ya yi alkawarin tabbatar da cewa “mugayen” ‘yan Najeriya za su fuskanci hukunci kamar doka ta tanada.

Tinubu ya gargadi masu aikata mugayen laifuka, ko suna cikin Najeriya ko waje, cewa za a gurfanar da su gaban shari’a.

Shugaban kasar, wanda mai ba shi shawara kan tsaro na kasa, Nuhu Ribadu, ya wakilta, ya yi wannan bayani yayin bikin kammala karatun Kwasa-kwasan Executive Intelligence Management Course 17 a cibiyar nazarin tsaro da ke Abuja a ranar Asabar.

Ya sake tabbatar da kudurin gwamnatinsa na tabbatar da tsaro da kwanciyar hankali a kasar.

“Idan kai mutum ne mara gaskiya, ko kana Najeriya ko kana waje, kana cikin matsala. Za mu bi ka. Za mu gurfanar da kai a gaban shari’a,” in ji shi.

Shi ma da yake magana, darakta janar na hukumar DSS, Adeọla Ajayi, ya bayyana cewa Najeriya ba za ta fuskanci matsalolin tsaro ba idan dukkan hukumomin tsaro suka yi aiki tare yadda ya kamata.

Ajayi ya ce, “Tare za mu yi nasara. CDS da NSA sun kawo hadin kai ta wata hanya da ban taba gani ba a tsawon aikina. Dole mu yi aiki tare.

“Darasinmu daga nan shi ne babu wata matsalar tsaro da za ta yi nasara a kanmu idan muka yi aiki tare.

“Ba da jimawa ba, duk ‘yan Najeriya za su rika yin barci suna rufe idanuwansu duka biyu. Godiya ga Shugaban kasa bisa irin shugabancin da kake ba wa kasar.

“Na gode da ka nada ni. Ba zan taba ba ka kunya ba.”

Za mu tabbata mugayen yan Najeriya sun fuskanci hukunci – Tinubu


Author: Gold Emmanuel
08 Dec 2024 @ 14:43pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.