Gold Emmanuel 2 weeks ago

John Mahama ya zama shugaban kasar Ghana

John Mahama ya zama shugaban kasar Ghana

Mataimakin Shugaban kasar Ghana kuma ɗan takarar jam’iyyar New Patriotic Party NPP mai mulki, Mahamudu Bawumia, ya amince da shan kaye a zaɓen shugaban ƙasar da aka yi karshen mako, bayan ya kira abokin hamayyarsa John Mahama don taya shi murna.

“Mutanen Ghana sun bayyana ra’ayin su , sun zaɓi sauyi a wannan lokaci kuma muna mutunta hakan da cikakken tawali’u,” in ji shi a wani taron manema labarai.

A shafinsa na X, zababben shugaban kasar John Mahama ya tabbatar da cewa ya karɓi kiran taya murna daga Bawumia.

Mataimakin shugaban ya ce Mahama ya lashe kujerar shugaban ƙasa “da babban rinjaye” hakazalika jam’iyyar adawa ta NDC ta lashe zaɓen majalisar dokokin ƙasar, bisa ga sakamakon ƙididdigar ƙuri’u na cikin gida na jam’iyyar NPP mai mulki.

Bawumia yayi ta kokari wajen nisantar da kansa daga suka kan yadda gwamnatin ta tafiyar da batun matsalar tattalin arzikin Ghana da tsadar rayuwa, waɗanda suka zama muhimman batutuwan da suka taka rawa a zaɓen.

 

John Mahama ya zama shugaban kasar Ghana


Author: Gold Emmanuel
08 Dec 2024 @ 14:43pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.