Gold Emmanuel 3 weeks ago

UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundin Al’adun Duniya

UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundin Al’adun Duniya

Hukumar kula da al’adu ta Majalisar Ɗinkin Duniya UNESCO ta sanya bukukuwan hawan daba da ake gudanarwa a Kano a lokutan sallar Idi cikin manyan al’adun duniya masu ɗimbin tarihi.

Hajo Sani wadda ke wakilatar Najeriya a UNESCO, ta bayyana bikin Hawan Dabar a matsayin bikin da ke nuna irin addo da martsba da kuma haɗin kan dake tsakanin al’ummar Kano.

Ta ƙara da cewar bikin na da matuƙar girman da ke janyo ƙabilu daban daban domin gabatar da al’adun su ciki harda Hausawa da Fulani da Larabawa da Nufawa da Yarbawa da kuma Abzinawa waɗanda da dama daga cikinsu sun rikiɗe sun zama al’umma guda a birnin.

An fara gudanar da hawan daba tun daga ƙarni na 15 Inda Sarki ke jagorancin tawagar da ta ƙunshi hakimai da fadawa da kuma mahaya dawakai sama da 10,000 waɗanda suka ci ado ana kuma buga musu tambura da busa algaita akan wasu titunan birnin.

Waɗannan bukuwan dai ana yinsu ne sau biyu a shekara, yayin bikin ƙaramar Sallah ko Eid el Fitr da babbar Sallah ko kuma Eid el Adha, a watan 10 na Shawwal da kuma Zul Hajj wato watan 12 na Islama.

Bikin al’adar Sukur da ake yi a kusa da iyakar Kamaru da kuma bikin al’adar mutanen Osogbo dake Jihar Osun suma sun samu shiga cikin jerin bukukuwan na UNESCO.

UNESCO ta sanya hawan Dabar Kano cikin kundin Al’adun Duniya


Author: Gold Emmanuel
06 Dec 2024 @ 09:36am
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.