Gold Emmanuel 3 days ago

Asibitin AKTH zai yiwa Yara 200 tiyatar burma hanci kyauta

Asibitin AKTH zai yiwa Yara 200 tiyatar burma hanci kyauta

Asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH) ya fara yi wa majinyata 200 tiyatar burma hanci kyauta a fadin kasar nan.

Aikin tiyatar wanda gidauniyar Qatar Charity Foundation ta dauki nauyin shi na da nufin rage radadin da kananan yara ke fama da shi da kuma ba su damar rayuwa mai inganci.

Da yake jawabi a wajen kaddamar da aikin tiyatar, Daraktan kasar a gidauniyar Qatar Charity, Hamdi Abdou ya ce “munyi nasarar gudanar da aikin tiyatar burma hanci ga dimbin yara a Pakistan, Somalia da Ghana. A yanzu mun himmatu wajen fadada wannan shiri a Najeriya, da nufin amfanar da kimanin yara 200 a fadin kasar nan.”

Ya ce ayyukan da gidauniyar keyi a Najeriya ya wuce aikin tiyatar burma hanci ta hada harda aikin ido da ginin asibitoci, tiyatar zuciya da tallafin kayan aikin likitanci na asibiti da sauran su.

“Dukkan wadannan yunƙurin na samuwa ne ta hannun ƙwaƙƙwaran jagoranci na Qatar Charity – Nijeriya da kuma ƙarƙashin jagoranci da goyon bayan Jakadan Qatar a Nijeriya, Dakta Ali bo Cihanem Al Hajri.” A cewarsa.

A nasa jawabin, Babban Daraktan asibitin koyarwa na Aminu Kano (AKTH), Farfesa Abdurahman Abba Sheshe ya bayyana cewa ana sa ran yin tiyatar yara 200 cikin watanni uku kyauta, yace za’a basu magani tare da ciyarwa yayin zaman jinyar da zasuyi kyauta.

Asibitin AKTH zai yiwa Yara 200 tiyatar burma hanci kyauta


Author: Gold Emmanuel
09 Dec 2024 @ 08:13am
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.