Gold Emmanuel 3 weeks ago

Amurka ta gargadi yan kasarta dake sha’awar zuwa kasashe Afrika 7

Amurka ta gargadi yan kasarta dake sha’awar zuwa kasashe Afrika 7

Ma’aikatar harkokin wajen Amurka ta sanya ƙasashe bakwai na Afrika a cikin matakin gargadi kan tafiye tafiye zuwa wadannan kasashe bisa ga rahoton binciken tsaro mai zurfi.

Kasashen sun haɗa da Libya, Mali, Somaliya, Sudan ta Kudu, Sudan, Burkina Faso, da Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya (CAR). Gargadin ya nuna barazanar rikice-rikicen da suka haɗa da yaƙi, da ta’addanci, da laifuka, da kuma rikicin cikin gida.

 

Rahoton ya bayyana cewa a kasar Libya rikici da ayyukan ta’addanci sun yi muni, yayin da a Mali ake fuskantar garkuwa da mutane da hare-haren ta’addanci, musamman wajen Bamako.

Somaliya na fama da laifukan kisan kai da garkuwa da mutane tare da barazanar hare-haren ta’addanci da fashin jiragen ruwa.

A Sudan da Sudan ta Kudu, rikici da sace-sacen motoci sun yi muni, tare da yawan kashe-kashe a Khartoum tun daga watan Afrilu 2023.

A Burkina Faso kuma, ta’addanci da rikici sun janyo dokar ta-baci a wasu sassan ƙasar. A Jamhuriyar Afirka ta tsakiya, galibin yankunan ƙasar na ƙarƙashin ikon kungiyoyin mayaka masu aikata laifuka da garkuwa d mmutane.

Amurka ta gargadi yan kasarta dake sha’awar zuwa kasashe Afrika 7


Author: Gold Emmanuel
02 Jan 2025 @ 20:38pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.