Gold Emmanuel 4 days ago

NSCDC ta buƙaci ƙarin haɗin kan hukumomin tsaro a 2025

NSCDC ta buƙaci ƙarin haɗin kan hukumomin tsaro a 2025

Babban kwamandan hukumar tsaron fararen hula ta Najeriya (NSCDC), Dakta Ahmed Audi, ya jaddada cewa raba bayanan sirri tsakanin hukumomin tsaro muhimmin mataki ne wajen samun nasarorin da aka cimma a manyan ayyuka don magance matsalolin tsaro a Najeriya.

Dakta Audi ya yaba wa ‘yan Najeriya kan raba muhimman bayanan sirri da hukumomin tsaro, yana mai cewa wannan tsari ya taimaka wa jami’an tsaro wajen cimma nasarori a kan rashin tsaro.

Baya ga yaki da ta’addanci ta hanyar dabarun yaki, garkuwa da mutane don karbar kudin fansa da kuma ‘yan fashin daji, shugaban NSCDC ya jaddada amfani da bayanan sirri daga ‘yan Najeriya wajen kare muhimmancin kadarorin kasa da muhimman ababen more rayuwa.

Ya ce rabon bayanan sirri tare da NSCDC ya taimaka wa hukumar wajen cika aikinta na kare kadarorin kasa da muhimman ababen more rayuwa.

Audi ya bayyana hakan ta bakin jami’in hulda da jama’a na hukumar, Babawale Afolabi, a cikin wata sanarwa da aka fitar a Abuja.

“Dakta Ahmed Abubakar Audi ya kuma gode wa ‘yan Najeriya masu kishin kasa da suka hada kai da hukumar don bunkasa aikinta da cika nauyin da doka ta dora mata,” in ji shi.

“Dakta Audi ya jaddada cewa mafi yawan nasarorin da hukumar ta samu da nasarorin ayyukanta sun dogara ne kan sahihan bayanan sirri da rahotannin da ‘yan Najeriya suka bayar wadanda suka amince da NSCDC a matsayin hukuma mai nagarta,” in ji jami’in hulda da jama’a.

Shugaban NSCDC ya kuma yaba wa dukkan kwamandojin jihohi, kwamandojin shiyya, da shugabannin hukumar kan nasarorin da aka samu zuwa yanzu.

Ya gode wa shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu, saboda samar da yanayi mai kyau da suka bai wa hukumar damar samun ci gaba.

Ya kuma yaba wa Ministan Harkokin Cikin Gida, Dakta Olubunmi Tunji-Ojo, saboda farfado da hukumar ta hanyar manufofi masu amfani da suka inganta nasarorinta da dama.

Ya kara jan hankalin jami’ai da ma’aikata da su guji duk wani abu da zai bata martabar hukumar.

Shugaban NSCDC ya sake tabbatar wa al’umma cewa hukumar za ta ci gaba da dagewa wajen yaki da satar danyen mai, ayyukan hakar ma’adanai ba tare da izini ba, lalata kayan gwamnati, da kuma kare rayuka da dukiyoyi baki daya, yayin da hukumar ke ci gaba da karfafa hadin gwiwa da sauran hukumomin tsaro don tsare kasar daga masu aikata laifuka.

NSCDC ta buƙaci ƙarin haɗin kan hukumomin tsaro a 2025


Author: Gold Emmanuel
01 Jan 2025 @ 17:12pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.