Gold Emmanuel 4 weeks ago

NNPC ta kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki

NNPC ta kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki

Kamfanin Man Fetur na Najeriya, NNPC ya bayyana sabbin bayanai dangane da shirin daukar ma’aikata da ake gudanarwa.

A ranar Asabar ne Kamfanin NNPC ya fara gudanar da jarabawar kwamfuta, CBT domin tantance masu neman aiki a wasu mukamai daban-daban a kamfanin.

Wannan mataki na daya daga cikin matakan daukar ma’aikata da kamfanin ke aiwatarwa don cike guraben aiki a bangarori daban-daban.

NNPCL ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook a ranar Asabar, inda ta nuna cewa mutane 45,689 ne ke neman guraben aikin da ake da su.

NNPCL ta bayyana cewa kawai wadanda suka fi cancanta za su samu damar cin gajiyar shirin daukar aikin da ake gudanarwa.

Shugaban Kamfanin NNPCL, Mele Kyari, wanda ya kai ziyara zuwa daya daga cikin cibiyoyin jarabawar, ya tabbatar da cewa za a gudanar da tsarin ne cikin sauki, gaskiya, adalci, da kuma sahihanci.

“A matsayin kamfani mai bayar da dama ga kowa, NNPC Ltd. ta tanadi wasu abubuwan musamman don tabbatar da cewa masu neman aikin da ke da nakasa za su iya shiga jarabawar ba tare da wata tangarda ba,” in ji Kyari.

A tunatarwa, a watan Yuli na shekarar 2024, mai magana da yawun NNPCL ya sanar da fara sabon shirin daukar ma’aikata.

NNPC ta kaddamar da jarabawar CBT ga masu neman aiki


Author: Gold Emmanuel
08 Dec 2024 @ 07:39am
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.