Gold Emmanuel 3 weeks ago

Kotu ta aike da Mahadi Shehu gidan Yari

Kotu ta aike da Mahadi Shehu gidan Yari

Babbar Kotun Majistare da ke zaune a Kaduna a ranar Talata ta ba da umarnin tsare fitaccen mai fafutuka kuma mai sharhi a kafafen sada zumunta, Mahdi Shehu a gidan gyaran hali na Kaduna.

Mahdi ya shiga hannun jami’an hukumar tsaro ta DSS kwanakin baya bayan ya ki janye wasu bidiyoyi da ya wallafa a yanar gizo, inda yake zargin cewa Shugaba Bola Tinubu ya ba wa Faransa izinin kafa sansanin soji a arewacin Najeriya.

Zargin da Mahdi ya yi ya zo ne bayan ikirarin shugaban mulkin soji na Jamhuriyar Nijar, Abdourahamane Tchiani, cewa Faransa ta kafa sansanin soji a arewacin Najeriya.

Amma dai mai ba da shawara kan harkokin tsaro na kasa, Malam Nuhu Ribadu, da kuma Ministan Labarai, Alhaji Mohammed Idris, sun musanta wadannan zarge-zarge, suna masu cewa ba su da tushe balle makama.

A ranar Talata, DSS ta gurfanar da Mahdi a gaban Mai Shari’a Abubakar Lamido bisa tuhume-tuhume biyu da suka hada da hadin baki, taimakawa da goyon bayan ta’addanci wanda ya sabawa Sashe na 26(2)(3) na Dokar yaki da Ta’addanci ta 2022, da kuma tayar da hankalin jama’a wanda ya sabawa Sashe na 78 na Kundin Dokokin Laifuka na Jihar Kaduna na 2017.

A hukuncinsa, Mai Shari’a Lamido ya yanke cewa Mahdi zai cigaba da kasancewa a gidan gyaran hali a Kaduna har zuwa ranar 14 ga Janairu, 2025, domin ci gaba da sauraron karar.

Bidiyon da Mahdi ya wallafa an riga an tantance su ta hannun gidajen jarida da dama, ciki har da Daily Trust da The Cable, inda suka gano cewa bidiyon sojojin Najeriya ne na 2013 da ke filin jirgin sama na Bamako, Mali, lokacin da suke kan hanyarsu ta shiga aikin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afirka a Arewacin Mali.

Kotu ta aike da Mahadi Shehu gidan Yari


Author: Gold Emmanuel
01 Jan 2025 @ 20:19pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.