Gold Emmanuel 3 weeks ago

Gwamnan Kano, Abba ya yi kakkausar suka kan ƙudirin haraji

Gwamnan Kano, Abba ya yi kakkausar suka kan ƙudirin haraji

Gwamnatin jihar Kano, da kakkausar murya ta yi watsi da kudirin garambawul ga dokar haraji da ke gaban majalisar dokoki a yanzu haka.

Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya maganta ta bakin mataimakinsa Aminu Abdussalam Gwarzo, ya bayyana matsayar gwamnatin ne a yayin bukin sabuwar shekara ta 2025.

Wata sanarwa da sakataren yaɗa labarai na mataimakin gwamnan Ibrahim Garba Shu’aibu ya fitar a yau Laraba, ta ce jihar Kano ba ta goyon bayan dokar saboda za ta shafi walwalar al’ummar ta

Tuni dai majalisar dokoki tayi wa dokar harajin karatu na biyu, sai dai an sake maida dokar ga ofishin antoni Janar na kasa domin sake yi mata garambawul biyo bayan yadda manyan Arewa da sauran al’umma suka nuna damuwa da tanade tanaden dokar

Gwamnan Kano, Abba ya yi kakkausar suka kan ƙudirin haraji


Author: Gold Emmanuel
01 Jan 2025 @ 20:19pm
Comments: 0


Disclaimer: The information contained in this content is for general purpose only and is generated from different sources other than MenBills Colony. Kindly report any fake news or false statement to support@menbills.com.ng

Comments (0)
There are no comments yet.
Comment

Leave A Comment
Please Sign In to be able to post a comment.